Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mata Hudu 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Sha Wuta


Yau an kashe wasu mata 'yan kunar bakin wake su hudu bayan da su ka ketara zuwa arewacin Kamaru daga Najeriya, a cewar wasu jami'an yankin.

Gwamnan yankin Arewa Mai Nisa na Kamaru, Midjiyawa Bakari ya gaya ma Muryar Amurka cewa 'yan banga ne su ka hango mata hudun na kokarin ketara kan iyakar da asubahin yau dinnan Laraba. Uku daga cikinsu sun tayar da bama-bamansu, su ka kashe kansu kawai, a yayin da ta hudun kuma sojoji su ka bindige ta har lahira a cewar gwamnan.

Ministan Sadarwar Kamaru wanda kuma shi ne mai magana da yawun gwamnati Issa Tchiroma ya gaya ma Muryar Amurka cewa sojojin kasar sun sha korar 'yan bindiga masu yinkurin ketara kan iyakar.

XS
SM
MD
LG