Dakarun dake biyaya ga kungiyar yan yakin sa kai ta Al Shabab a Somaliya sun kaiwa wani wurin binciken sojan Somaliya hari suka kashe akalla mutane tara.
Jami’an Somaliya dana kungiyar Al Shabab sunce a ranar juma’a da dare zuwa safiyar jiya asabar aka yi wannan fafatawa a kusa da Bosasso a yankin Puntland.
Mai magana da yawun rundunar sojan Al Shaba Sheikh Abdiasis Abu Musab ya fadawa kafofin yada labaru cewa, dakarun kungiyarsa sun kai hari, kuma sun kashe sojojin gwamnati guda talatin. To amma wani jami’in yankin ya fadawa kamfanin dilancin labarun Reuters cewa mutane tara ne kurum aka kasha, kuma biyar daga cikin wadanda aka kasha ‘yan yakin sa kai ne.
Tarzomar baya bayan nan ta barke ne a yayinda sojoji Somaliya dana Ethiopia da kuma wasu sojojin da kungiyar kasashen Afrika ke marawa baya suka yi ikirarin cewa suna samun nasarar a fafatawar da suke yi da kungiyar Al Shabab.