Kasar Ghana na bukin zagayowar ranar samin ‘yancinta daga kasar Burtaniya karo na 55 da irin faretin da aka saba a Accra babban birnin kasar da kuma jawabi daga Shugaba John Atta Mills.
Babban bukin da ake yi a yau Talata a babban Dandalin ‘Yacin Kai da ke Accra za a yi irinsa a yankuna da kuma hedikwatocin gundumomin kasar.
Ministan Harkokin Gidan Ghana Fritz Baffour ya gaya wa Muryar Amurka cewa wannan wata dama ce ta sabunta damar da kasar ta samu.
Bayan shagulgulan samun ‘yancin kai, Shugaba Mills zai ziyarci Amurka, inda zai gana da Shugaba Barack Obama ranar Alhamis a Fadar White House.
Ministan Cikin Gidan ya gaya wa Muryar Amurka cewa yana kyautata zaton ziyarar za ta karfafa dangantakar Amurka da Ghana, kuma wannan ziyarar za ta amfani ‘yan Ghana.
Mr. Obama ya ziyarci Ghana a 2009 a ziyararsa ta farko zuwa Afirka kudu da Sahara a matsayinsa na Shugaban kasa. Ya ce ya tafi Ghana ne don ya karfafa tsarin dimokaradiyyarta.