Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Al Shabab Ta Ce Ta Kai Hare-hare Kenya Da Somaliya


Kungiyar Al Shabab mai ra’ayin rikau ta kasar Somaliya tace ta kai hare hare guda uku a kasashen Kenya da Somaliya jiya Laraba harma ta kashe mutane goma sha shidda yawancinsu yan sanda da jami’an tsaro.

Kwanan nan gwamnatin Somaliya ta kaddamar da sumamen murkushe yan kungiyar kuma jami’an kasar Kenya sun ce yan yakin sa kan kungiyar suna dandanawa daga wannan mataki.

Jami’ai a birnin Mogadishu sunce akalla mutane takwas aka kashe, sha biyar kuma suka ji rauni a sakamakon tashin wani bam da aka boye cikin wata mota kusa tashar jiragen ruwan kasar

A kasar Kenya kuma, shedun gani da ido sunce jami’an tsaro guda takwas aka kashe a tashin bama bamai guda biyu dabam dabam da aka boye a gefen hanya a arewa maso gabashin kasar kusa da kan iyakar kasar da Somaliya.

A can kasar Indonesia ma, wasu hare haren kunar bakin wake sun girgiza wata tashar mota a Jakarta baban birnin kasar jiya Laraba, suka kashe akalla jami’an yan sanda guda uku.

Wasu jami’an yan sanda biyar da farar hula biyar ne suka ji rauni a hare haren. Ba’a dai tantance kungiyar da ke da alhakin kai hare haren ba. Amma a baya kungiyar ISIS tayi ikirarin kai hare hare makamancin wannan a kasar data fi kowace kasa yawan Musulmi a duniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG