Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar al-Qaida Ta Rasa Wani Shugabanta a Yemen


 Al-Qaida da ISIS
Al-Qaida da ISIS

Sanadiyar hare-haren da Amurka ta kai Yemen kungiyar al-Qaida ta rasa wai babban shugabanta Nasir Ali al-Ansi

A Yemen, kungiyar al-Qaida dake kasar tace wani harin da Amurka ta kai da jiragen yaki cikin watan jiya ya kashe daya daga cikin manyan shugabanninta.

Wani dandalin masu aikin leken asiri da ake kira SITE ya bada rahoto jiya Alhamis cewa reshen al-Qaida a Yemen ya ce wani farmaki ta sama da Amurka ta kai a birnin da ake kira Mukalla mai tashar jiragen ruwa ya kashe Nasser bin Ali al-Ansi, da babban dansa da wasu mayakan sakai.

Ansi a madadin kungiyar al-Qaida a makurdin Arabiya ya dauki alhakin harin da 'yan ta'adda suka kai kan ofishin mujallar Charlie Hebdo wacce take amfani da zane wajen barkwanci da yin ba'a ga addinin Islama.

A wani taro da manema labarai saktaren tsaron Amurka Ashton Carter yaki yace kome kan wannan rahoto. Yace "bama magana kan wannan, musamman dai daga inda yake tsaye. Gameda kungiyar al-Qaida a zirin Arabiya yace suna ci gaba da matsin lamba a can.

XS
SM
MD
LG