Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Tsarin Mulkin Nijer Ta Bayyana Sakamakon Zaben Watan Disamba


Kotun tsarin mulkin jamhuriyar Nijer ta bayyana sakamakon dindindin na zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 27 ga watan Disamba da ya gabata, sai dai kotun ta ce daga cikin ‘yan takara 30 da suka fafata a zagayen na farko ba wanda ya sami sama da kashi 50 daga cikin 100 na kuri’u.

Bayan shafe makonni 4 ta na nazarin sakamakon wucin gadin da hukumar zabe ta gabatar wa kotun tsarin mulkin kasa ne alkalan kotun suka yi wani zama a cikin daren ranar Asabar domin sanar da jama’a abubuwan da suka gano a game da zaben na ranar 27 ga watan Disamba.

Shugaban kotun ta Cour Constitutionelle mai shari’a Bouba Mahaman, ya ce daga cikin mutane miliyan 7 446556 da suka yi rajistar zabe, miliyan 5189132 ne suka halarci runfunan zabe, wato kashi 69.68 daga cikin 100 kenan.

Dan takarar jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki Bazoum Mohamed ne ke kan gaban wadannan ‘yan takara da kuri’u miliyan 1.879629, sai dan takarar jam’iyyar RDR Canji ta ‘yan adawa Mahaman Ousman mai kuri’u 812412, sannan sai Seini Oumarou na MNSD Nassara da Albade Abouba na MPR Jamhuriya da ke rufa masu baya.

Kotun ta ce kasancewar babu dan takarar da ya sami sama da kashi 50 daga cikin 100 na kuri’un zabe ya sa dole a je zagaye na 2 domin raba gardama a tsakanin Bazoum Mohamed da Mahaman Ousman.

Kwanaki kadan bayan da hukumar zabe ta fitar da sakamakon wucin gadi, wasu daga cikin ‘yan takarar jam’iyyun hamayya da suka hada da Mahaman Ousman da Ibrahimm Yacouba, sun shigar da kara a gaban kotun tsarin mulkin kasa a bisa zargin tafka magudi a wasu wurare yayin da suka ce a wasu yankunan ba a gudanar da zaben ba ko kuma ya gudana cikin wani yanayi na rashin mutunta doka. Sai dai kotun ta yi watsi da wadannan korafe-korafe.

Bayyana wannan sakamako ke da wuya kai tsaye magoya bayan ‘yan takarar 2 suka soma haramar yakin zabe da nufin samun yardar talakawa a karon da za a yi tsakanin Mahaman Ousman da Bazoum Mohamed a ranar 21 ga watan Fabarairu.

Saurari cikkaken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

XS
SM
MD
LG