Yayin da kotun kolin Amurka ta zartar da wasu hukunce-hukunce akan Shugaba Donald Trump game da kin bada wasu takardun harkokin kudadensa, yanzu muhawarar da ake yi a kasar ita ce ko babban hukuncin da aka yanke nasara ce ko akasin haka ga Trump.
Dukkan hukunce-hukuncen da kotun ta yanke a ranar 9 ga watan Yuli sun tabbatar da cewa ba za a saki takardun haraji da sauran wasu bayanan harkokin kudin Shugaban da ya yi ta kaffa-kaffa da su ga jama’a ba, da ta yiwu abokan adawar sa su sami abin caccaka kafin zaben ranar 3 ga watan Nuwamba.
Amma matakin babbar kotun ya yi watsi da ikirarin da Trump ya dade ya na yi akan yana da kariya ba zai bada bayanansa ba da kuma tunanin sa game da ikon shugaban kasa.
Kotun ta ce babu wanda ya fi karfin doka a Amurka, ciki har da Shugaban kasa.
A dayan bangaren kuma kotun ta ce yayin da Majalisar Dokokin kasar ke da ikon bukatar wasu bayanai daga Shugaban kasa wannan ikon na da ka’ida.
Facebook Forum