Yau Alhamis kotun kolin Amurka ta baiwa shugaba Barack Obama gagarumar nasara, ta yanke hukuncin amincewa da muhimmin sashe na dokar garambawul ga dokar kiwon lafiya da ya jnayo gardama.Alkalai 5 suka amince da dokar hudu kuma suka ki amincewa.
Karkashin dokar, tilas Amurkawa su sayi inshorar kiwon lafiya nan da 2014, ko kuma su biya haraji. Alkalin alkalan Amurka mai shari’a John Roberts yayi jam’u da alkalai masu sassaucin ra’ayi, a hukuncin da ya rubuta a madadin kotun, mai shari’a Roberts yace tsarin mulki ya amince da irin wan nan haraji, sabo da haka ba hurumin kotun bane ta haramta shi ko kuma ta yanke hukunci kan dacewa ko sabanin haka kan hikimar dokar.
Alkalan kotun koli Stephen Breyer, da Ruth Baderginsburg, da Elena Kagan, da Sonya Sotomayor, sune saura hudun da John Roberst da suka goyi bayan dokar.
Da yake magana bayan kotun ta yanke hukuncin, shugaba Obama yace wan nan huuncin babbar nasara ce ga Amurkawa bakin daya.