An same Lawan, wadda tsohon shugaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai kan tallafin man fetur ne, da laifi kuma aka yanke masa hukuncin dauri zuwa gidan yari a shekarar 2021 saboda karbar cin hancin $500,000 daga hannun dan kasuwa Femi Otedola, shugaban kamfanin Zenon Petroleum and Gas Limited.
Shari’ar da ke ci gaba da gudana tun a shekarar 2013, ta kai ga gaci a yayin da kotun koli ta tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja, ta yanke wa Lawan, hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari, tare da gurfanar da shi a kan laifuka biyu daga cikin uku na cin hanci da rashawa.
A hukuncin da mai shari’a John Okoro ya shirya kuma mai shari’a Tijjani Abubakar ya karanta, kotun koli ta amince da cewa karar da Lawan ya shigar ba ta da inganci sannan ta yi watsi da shi.
Kwamitin mutum biyar ya tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a shekarar 2022, inda ya tabbatar da hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari kan Lawan dangane da tuhume-tuhume uku da ya fuskanta a babbar kotun birnin tarayya.
Fadi tashin shari’ar Lawan ta fuskanci dambarwa daban-daban. Da farko dai, kwamitin mutane uku na Kotun Daukaka Kara, karkashin jagorancin Monica Dongban-Mensem, ya yi watsi da hukuncin Lawan kan laifuka biyu daga cikin ukun da aka yanke masa, inda daga baya ya rage zaman gidan yari daga shekaru bakwai zuwa biyar.
Sai dai kuma, Lawan ya ci gaba da zama da laifi a kan laifuka na uku, wanda ya sa aka daure shi na shekaru biyar na karshe.
A yayin zaman sauraron karar da aka yi a kotun koli, Lauyan Lawan mai matsayin SAN, Joseph Daudu, ya bayar da hujjar yin watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, yana mai jaddada sabanin da ke tattare da tuhumar.
A daya bangaren kuma, Lauyan gwamnatin tarayya, Bagudu Sanni, ya bukaci kotun da ta tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke tare da yin watsi da karar da Lawan ya shigar.
Shari’ar da ake wa Lawan ta samo asali ne daga zargin neman cin hancin dala miliyan 3 daga Femi Otedola a yayin binciken badakalar tallafin man fetur na biliyoyin naira a shekarar 2012 na kamfanonin mai da ke da hannu a badakalar.
A cikin lokaci mai tsawo, Mai shari’a Angela Otaluka na babbar kotun birnin tarayya ta yanke wa Lawan hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari bisa samunsa da laifin zarge-zarge na daya da biyu, da kuma shekaru biyar kan laifuka uku.
Mai shari’a Otaluka ya jaddada hujjojin da masu gabatar da kara suka gabatar da kuma yadda Lawan ya kasa bada hujjar karbar cin hancin a matsayin shaida a gaban Kotu.
Zuwa yanzu dai hukuncin Kotun Koli dai ya kawo karshen shari’ar da ake yi wa Lawan yayin da aka kai shi gidan yari domin cika wa’adinsa na shekaru biyar.
Masu sharhi a fagen shari’ar Najeriya da dama sun yaba, kuma suna ganin irin wannan hukuncin ya nuna wani gagarumin mataki na yaki da cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da doka a fagen shari’ar Najeriya.
~ Yusuf Amin Yusuf
Dandalin Mu Tattauna