Jiya kotun daukaka kara ta gwamnatin tarayyar Najeriya ta yanke hukuncin karar dake gabanta inda ta mayarda sarkin Yamaltu Alhaji Ibrahim Muhammad Bello kan karagar mulkin masarautarsa dake jihar Gombe.
An shafe shekaru goma sha daya ana gudanar da shari'a akan shigeshin da aka yi.Barrister Alhassan Aliyu Sange shi ne lauya mai wakiltar sarkin ya kuma kara bayani.
Yace kotun ta ce gwamnatin wancan lokacin a karkashin Danjuma Goje ta kori sarki ne ba tare da wani dalili ba. Saboda haka kotun ta mayar dashi kan mulki. An yi korar ne ba tare da bin tsarin mulkin Najeriya ba . An yi ganin dama ne aka koreshi.
Kotun tace a hada sarkin Yamaltun da na Akko kowannesu ya koma fadarsa. Alkalai uku a karkashin Mai Shari'a Jummai Hannatu Sanke suka yanke hukuncin.
Duk wanda bai gamsu da hukuncin ba na iya daukaka kara zuwa kotun koli.
Dangane da mayarda sarkin Akko lauyan yace suna samun tutsu da tirjiya daga wadansu da suke kusa da gwamnatin jihar Gombe. Yace idan lokaci yayi zai fadi sunayensu kuma zasu dauki matakan da suka dace.
Sarki Ibrahim Muhammad Bello ya godewa Allah da ya bashi nasara a kotun.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.