Babbar kotun laifukka ta duniya ta ICC tace a ranar litinin ne zata yanke hukunci akan ko za’a gurfanar da wadansu manyan kusoshin kasar Kenya a gabanta domin su amsa laifukkan da ake zarginsu da aikatawa na keta hakkin bil adama.
A yau Jumu’a ne wannan kotun dake birnin Hague take fadar cewa zata shirya zaman bainar-jama’a don jin ko akwai isasshiyar shedar yi wa mutanen wannan shara’a.
Su dai wadanan mutanen shidda, da suka hada da kusoshin gwamnati ta yanzu da ‘yan kasuwa, ana zarginsu ne da laifin kitsa rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar Kenya na shekarar 2007 wanda a cikinsa aka hallaka mutane kamar 1,300 yayinda wasu fiyeda 300,000 suka rasa muhallinsu