Amurka tana kira ga Afirka ta kudu ta taimaka wajen hana aukuwar bala’in ‘yunwa a Sudan.
Jakadan Amurka na musamman zuwa Sudan Princeton Lyman, yace farar hula a kudancin jihar Kodofan da Blue Nile suna fuskantar karancin abinci. A lokacin wani taro da manem alabarai a Pretoria yau laraba, jakadan yayi kira ga Afirka ta kudu ta matsawa Khartoum lamba ta kyale kungiyoyin agaji na kasa da kasa su kai ga yankin.
A jiya talata ma Amurka tayi wan nan gargadi ga kwamitin sulhu a wasikar da ta Washington din ta rubuta, wasikar da Muriyar Amurka ya sami kopi. Cikin wasikar Amurka ta zargi Sudan da hana kungiyoyin agaji kaiwa ga wadan nan jihohi, inda gwamnatin take fafatawa da ‘yan tawaye tun a tsakiyar bara.
Jakadan Sudan a MDD ya fada jiya talata cewa babu wata matsala dangane zamanta- kewar mutane cikin jihohin nan biyu, kuma Sudan bata hana kungiyoyin agaji kaiwa ga jihohin ba.