Dokar da idan ta fara aiki zata shafi wata mata da 'yarta daga Aleppo wajen shigowa Amurka a matsayin yan gudun hijitra domin samun mijinta da tuni shi ya riga ya sami shigowa bayan an bashi damar zaman gudun Hijira a Wisconsin.
Alkalin kotun wato William Conley ya gabatar da tsaikon dokar na wucin gadi a jiya Juma’a wacce za ta yi aiki akan matar kadai da 'yarta kadai don haduwa da mijinta anan kasar Amurka.
Sabuwar dokar ta Trump zata fara aiki ne a ranar 16 ga watan Maris. amma an shirya tafiyar uwar zuwa Jordan inda za ayi mata tambayoyi domin buga mata biza a ofishin jakadancin Amurka a can. Wanda hanyoyin da za’a bi za su wuce kwanakin da aka dibarwa dokar ta fara aiki.
Conley yace mijin ya gabatar da hujjoji masu karfi da suka tabbatar da bukatarsa ta ganin iyalansa, wanda yace yana da matukar hadari da kuma cutarwa idan aka tilasta musu da su tsaya a Syria.
Idan ba’a manta ba a farkon wannan shekarar Trump ya gabatar da Dokar wucin gadi ta hana 'yan wasu kasashe bakwai shigowa Amurka da mafiya yawansu na Musulmi ne.
Wadanda suka hada da Iran da Iraqi da Libya da Somaliya da Sudan da Siriya da kuma Yamal. An murkushe wannan doka bayan Jihar Washington tayi nasarar hana dokar aiki da Kotun gwamnatin tarayya tayi.
A sabuwar dokar da aka gyara an cire kasar Iraqi daga cikin jerin sunayen kasashen da aka haramtawa shigowa Amurka na wucin gadi da kuma wasu 'yan gyare-gyare.
Facebook Forum