Tun a watan Yunin shekarar 2016 ne hukumar EFCC ta gurfanar da babban Hafsan a kotu kan tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa da ya hada da karbar dalar Amurka $300,000 da kuma karin wasu Naira Miliyan 5.9.
Hukumar EFCC ta na kuma tuhumar Alkali Mamu da karbar kyautar motoci biyu kirar ‘Ford Expedition suv’ da kudinsu ya kai Naira Miliyan 15, sai kuma wata mortar kirar ‘Jaguar XF saloon’ da ita ma kudinta ya kai Naira Miliyan 12, daga wani kamfani mai Suna ‘Society D'Equipments internationaux Nigeria limited’ lokacin da wannan kamfani ke neman kwangila.
Bayan da aka ja doguwar muhawara tsakanin lauyoyin bangarorin biyu, Alkalin kotun mai shari'a Salisu Garba, ya ce hukumar EFCC ta gaza gabatar da kwararan shaidu da za su gamsar da kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifuka hudun da ake zarginsa da su.
Sannan hukumar ta EFCC ta kuma gaza gabatar da wani shaida mai suna Abubakar a gabanta, duk da cewa a lokacin da EFCC ke gudanar da binciken ta na sane cewa shi Abubakar din yana Jamhuriyar Nijar, Amma ta kasa gayyato shi.
Lauyan wanda ake ‘kara Mista Adedayo Adedeyi, ya ce ya gamsu da hukuncin da aka zartas na wanke wanda suke karewa don ba bu isassun kuma gamsassun shaida da za a iya dogara kansu bisa tuhume-tuhumen da EFCC ke masa.
Muryar Amurka ta ji ta bakin shi Air vice Marshall Alkali Mamu, Inda ya bayyana godiya ga Allah bisa wannan hukuncin da aka yanke, yana mai kaddamar cewa dama kotu ita ce madogara ta karshe ga duk wanda ake son a zalunta.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum