Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Saki Wasu ‘Yan Jam’iyyar Adawa Da Aka Tsare A Jamhuriyar Nijar


Sumana Sanda Dan Adawar gwamnatin Nijar
Sumana Sanda Dan Adawar gwamnatin Nijar

A jamhuriyar Nijar kotu ta sallami wasu ‘yan adawa su kimanin 6 cikinsu har da dan Majalisar dokokin ‘kasar Sumana Sanda, jigo a jam’iyyar MODEN LUMANA bayand a suka shafe watanni sama da 10 a gidan yari saboda zarginsu da yunkurin shirya tarzoma ta hanyar amfani da makami zargin da ‘yan adawa suka sha musantawa.

Dubban magoya bayan jam’iyyar MODEN LUMANA sun hallara a kofar cibiyar wannan jam’iyyar domin tarbar shugaban reshen Yamai Sumana Sanda da abokansa biyar, wandanda hukumomin Nijar suka garkame tun ranar 14 ga watan Nuwambar 2015.

A lokacin da yake jawabi Sumana Lumana ya tuna da sauran jiga jigan jam’iyyun adawa kusan 20 da ake ci gaba da tsarewa yanzu haka.

Zaman doya da manya da tsakanin magoya bayan MODEN LUMANA da gwamnatin jamhuriya ta bakwai ya samo asali ne tun bayan da Hamma Amadu da makarrabansa suka ki karbar mukaman da shugaba Isoohu ya basu a gwamnatin da ya kafa a watan Agustan 2013, suna masu cewa fanko ne aka basu, a cigaban wannan takaddama jam’iyyar MODEN LUMANA na zargin masu mulki da bita da kullin siyasa akan ‘ya ‘yan ta, yayin da jam’iyya mai mulki PNDS ke cewa wannan korafi bashi da tushe.

Saurari rahotan Sule Muminu Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

XS
SM
MD
LG