Mai shari'a Ijeoma Ojukwu ta babbar kotun tarayya a Abuja ta bada belin tsohon mai bai wa shugaban kasa shawarar kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki akan Naira miliyan dari biyu da kuma samun mai tsaya masa wanda ya kasance ma'aikacin gwamnati da bai gaza matakin albashi na 16 ba, sannan a samu wani babban mutum wanda ke da mallakar kaddara nan Abuja.
Mai shari'ar ta nuna bacin ranta kwarai ga yadda aka yi ta bada belin Dasuki amma gwamnatin Najeriya ta ki bin umarnin kotu.Kotun ta yi watsi da ikirarin gwamnatin cewar ana ba shi kariya ne a wani wuri na musamman mai cike da tsaro saboda an samu makamai a gidansa.
Haka zalika mai shari'ar kuma ta yi watsi da karin hanzarin da gwamnatin Najeriya ta bayar cewar, ana ci gaba da tsare Dasuki saboda wasu karin tuhume-tuhume da ake masa.
"Ina kira ga gwamnatin tarayyar ta zamanto mai girmama hukunci da kuma umarnin kotu." inji lauya mai kare Dasuki, Barista Ahmed Raji
Iyalen Dasuki suna fatan gwamnatin Najeriya za ta mutunta wannan hukuncin kotu.
"Akan haka muna fata gwamnati za ta yi amfani da wannan ikirarin da ta ke yi na cewa tana bin doka, ta bi hukuncin bada shi beli," inji mai magana da yawun iyalen, Sanata Ummaru Dahiru Tambuwal.
Kokarin jin ta bakin gwamnatin Najeriya bai yi nasara ba.
A baya dai, kotuna dabam-dabam har da kotun Afirka ta yamma sun yanke hukuncin bada belin Kanal Sambo Dasuki amma gwamnatin Najeriya ta yi mursisi, ta ki bin umarnin. Yanzu dai, abin jira a gani shine, ko gwamnatin za ta bi wannan umarnin kotun na baya-bayannan?
Saurari rohoton Hassan Maina Kaina
Facebook Forum