Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya ta gurfanar da shugaban majalisar wakilan kasar Alhassan Ado Doguwa a gaban kotun majistire ta jihar.
Ana tuhumar Doguwa da hannu a tarzomar zabe, inda wasu mutane uku suka rasa rayukansu a yankin mazabarsa.
Alkalin kotun mai shari’a Ibrahim Mansur Yola ya ba da umurnin tsare Alhassan Ado a gidan kurkuku ko cibiyar gyaran hali ta Goron Dutse da ke birnin Kano.
Daga bisani, alkalin ya dage saurarn karar zuwa ranar 7 ga wannan wata na Maris lokacin da kawo batun neman a ba da shi beli.
A shekaranjiya litinin ne tarzoma ta barke a garin Tudunwada tsakanin magoya bayan jam’iyyun APC da NNPP, al’amarin da yayi sanadiyyar mutane akalla uku yayin da wasu da dama suka jikkata.