Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Kwato Wa Wasu Gomman Talakawa Hakkinsu Daga Hannun Shugaban Karamar Hukumar Kuje 


Kotu
Kotu

Biyo bayan kwashe sama da watanni 30 da ci gaba da zirga-zirgar neman kotu ta kwato musu filayensu na kasuwanci da aka kwace ba bisa kai’da ba, wata babbar kotun tarayya dake zamanta a yankin Kuje na birnin Abuja, ta zartar da hukuncin kwato masu hakkinsu.

ABUJA, NIGERIA - Babbar kotun ta kuma bada umarnin cewa wanda ake kara ya biya diyyar zirga-zirgar kotu na Naira miliyan 10 ga wadanda suka shigar da kara tare da mayar musu da filayen kasuwancinsu da aka kwace.

A ranar 4 ga watan Yulin shekarar 2020 ne wasu masu kananan sana’o’in da aka kwace wa filayen da suke gudanar da kasuwancinsu na yau da kullum, suka shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya dake da zama a yankin Kwali na birnin tarayya Abuja, inda suka kwashe sama da watannin 30 suna zirga-zirgar zuwa kotu domin neman a kwato musu hakkinsu da aka take ba bisa ka’ida ba.

Wannan batun dai ya sanya akasarin masu kanana sana’o’in cikin mawuyacin halin inda lamarin ya yi sanadin mutuwar hudu daga cikinsu.

A yayin zartar da hukuncin da aka yi a kotun Kuje wanda ya bai wa gomman masu kananan sana’o’in nasara, mai shari’a, Hon. Justice V. S. Gaba ya yi watsi da bukatar wanda ake kara da ya yi wa kotu rantsuwa a bisa karya na cewa bai rushe wajen kasuwancin masu karamin karfi da suka shigar da kara ba, wanda daga bisani kotu ta gano gaskiyar lamarin a bisa bincikenta kafin zartar da hukunci a yau Alhamis, 26 ga watan Janairun 2023.

Wasu daga cikin gomman mutanen da al’amarin ya shafa sun nuna farin cikinsu a game da hukuncin kotu da ya basu nasara, suna masu cewa kotu ta sake karfafa musu gwiwa a kan yiyuwar a sami gyara a batun nema wa talakawa hakokkinsu idan aka zalince su.

Abdulrahman Ali sarkin magina a yankin Kuje na birnin Abuja, ya ce abun da shugaban karamar hukumar Kuje ya yi bai dace ba kasancewar an kafa hukumar ne don taimakon talaka ba wai a yi musu zalunci ba, ya kara da cewa alkalan da suka zartar da hukunci a kań wannan al’amari sun yi daidai, kuma ya ce idan har ana yin daidai kamar yadda aka kwatanta a wannan hukunci, Najeriya zata gyaru.

Alex Zira Teru lauyan da ya kare gomman talakawa da aka zalunta a kotun ya yi bayani a kan abun da ya wakana a kotun da ta bai wa wadanda ya ke karewa nasara da damar su koma kan filayen kasuwancinsu.

A babbar kotun yankin Kwali aka fara zaman sauraron wannan shari’a inda daga bisani aka maida ta yankin Kuje da ya kai ga zartar da wannan hukuncin.

Idan ana iya tunawa, a cikin makon da ya gabata ne wasu masu ruwa da tsaki a bangaren shari’a suka sake jaddada mahimmancin a rika yin adalci ta fuskar shari’a don dawo da martabar Najeriya a idon duniya.

Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf:

Kotu Ta Kwato Wa Wasu Gomman Talakawa Hakkinsu Daga Hannun Shugaban Karamar Hukumar Kuje .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

XS
SM
MD
LG