Gwamnatin Turkiyya ta fadi cewa Mallam Gulen, wanda yake tsohon abokin shugaba Recep Tayyip Erdogan ne, shine madugun juyin mulkin tare da wasu jami’an sojan kasar, kuma ta yi kira ga Amurka da ta mayar da shi Turkiyya. Har yanzu dai babu wani mataki da Turkiyyar ta dauka a hukumance na ganin Amurka ta mayar da shi.
Mallam Gulen dai ya musanta cewa yana da hannu, ko yana da wata masaniya dangane da kokarin juyin mulkin kafin kafin ranar 15 ga watan Yulin wannan shekara, ya kuma yi Allah wadai da juyin mulkin.
A lokacin da yake magana da shugabannin ‘yan kasuwa a birnin Ankara jiya Alhamis, Erdogan yace “gwamnatinsa zata yanke hulda da duk wani kamfani da yake hulda da mallam Gulen, wacce tayi sanadin mace-macen mutane
Ya kuma ‘kara da cewa “duk sisin kwabon da yaje asusun kungiyar Mallam Fethulla Gule ta yaki da ta’addanci da ake kira FETO, zai zamanto harsashi ne da za a iya amfani da shi wajen yakar Turkiyya.”