Ministar Kula da Harkokin Mata Dame Pauline Talen ta ce gwamnati tana kokarin ganin Majalisa ta amince da wannan bukata kafin zaben shekara 2023.
Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Women in Politics a turanci, ita ce ta shigar da kara inda ta bukaci a aiwatar da kashi 35 cikin 100 na nadin mata a mukaman gwamnati.
Mai shari'a Donatus Okworonkwo ya amince da bukatar su, inda ya yanke hukuncin ba mata kashi 35 cikin 100.
Okoronkwo ya ce mata sun dade suna fama da wariya a fanin mukamai na gwamnati a Najeriya saboda haka,lokaci ya yi da ya kamata a cika masu burin su.
A lokacin da yake jawabi a game da hana mata taka rawa a fagen siyasa da kuma hana su izinin rike mukaman gwamnati a adinance, Alhaji Atiku Walin Kalgo ya ce ba daidai ba ne.
Shi ma Pastor James Movel Wuye ya ce babu inda addinin Kirista ya hana mata shiga siyasa ko samun mukaman gwamnati.
A shekara 1995 ne Najeriya ta rattaba hannu a yarjejeniyar ba mata kashi 35 cikin 100 na mukamai a taron da suka yi a Beijing kasar China, amma har ya zuwa yanzu mata ba su taba samun wannan kason a Najeriya ba.
Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda: