Jiya juma’a tsohon sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan, wanda shine wakilin kungiyar kasashen Larabawa da Majalisar Dinkin Duniya akan Syria, yayi kira ga wakilan kwamitin sulhu na Majalisar da su magance cijewar da suka samu akan matsawa Syria lamba dangane da murkushe yan tawaye da take yi.
A bayanin da yayi daga Geneva, Kofi Annan yace a makon gobe idan Allah ya kaimu zai tuwa wata tawaga zuwa Syria domin tattauna shirin tura masu lura na kasa da kasa. Mr Annan yayi wannan furuci ne a lokacinda ya yiwa kwamitin sulhu bayani ta hoto vidiyo a jiya juma’a, kasa da mako guda bayan ganawar da yayi da shugaba Bashar Al Assad na Syria.
Bayan bayanin nasa ne Mr Annan ya fadawa yan jarida cewa tilas a tinkari al’amarin na Syria cikin taka tsan tsan, domin kuwa, dan kuskure kadan idan akayi, to kamarin al’amarin ko kuma tarzomar zata shafi ilahirin yankin.
Jiya juma’a kafofin yada labarun Syria suka gabatar da wata sanarwa, kafin Mr Annan yayi nasa bayani. Sanarwar tace gwamnatin Syria tayi alkawarin baiwa Mr Annan hadin kai domin a samu hanyar magance wannan rikici a siyasance. A sanarwar ma’aikatar harkokin wajen Syria ta sake dora laifin yawancin rikicin kasar akan yan ta’ada da kuma shishigin wasu kasashen duniya.
A ranar asabar da lahadi, Kofi Annan ya gana da shugaba Assad. Ya kuma gabatar masa da shawarwarin kawo karshen fafatawar.
Jiya juma’a tsohon sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan, wanda shine wakilin kungiyar kasashen Larabawa da Majalisar Dinkin Duniya akan Syria, yayi kira ga wakilan kwamitin sulhu na Majalisar da su magance cijewar da suka samu akan matsawa Syria lamba dangane da murkushe yan tawaye da take yi.
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024