Yayin da masu zuba jari ke ci gaba da fatan alheri kan farfadowar tattalin arzikin Amurka, kasuwar hannayen jarin Amurka ta fuskanci tashin gwauron zabi a jiya Laraba.
Kasuwar Dow Jones ta tashi da maki 533 ko kuma da kashi 2. Hakan ya sa Dow Jones ta rufe da maki 25,000, wannan ne karo na farko tun lokacin da coronavirus ta fara gigita kasuwannin a watan Maris, da aka samu hakan.
Kasuwar S &P 500 Da Kuma NASDAQ indexes, dukkaninsu sun tashi da kashi 1.
Wadannan nasarorin da aka samu ya biyo bayan mikewa da hannayen jarin bankuna su ka yi, wani mataki mai nuna yadda masu zuba jari suke da kwarin gwiwa kan farfadowar tattalin arzikin kasar.
Amma kamfanonin da ke samun ci gaba idan mutane suna zaune a gida, kamar zoom da amazon sun fadi.
Facebook Forum