Kasuwar hadahadar kudade ta duniya ta fara fuskantar koma-baya a makon da ya gabata, yayin da matsalar da tattalin arzikin Turkiyya ke fuskanta, ta haifar da sabuwar fargabar cewa akwai yiwuwar tasirin komadar tattalin arzikin kasar, ya fadada har ya kai ga karayar tattalin arzikin duniya, kamar yadda aka gani a shekarar 2008.
Farashin hannayen jarin bankunan nahiyar turai da manyan masu bai wa Turkiyya bashi, sun fadi warwas, sannan kudaden China, Brazil da Mexico duk sun raunana.
Masu fashin baki da dama na fadin cewa, babban tasirin komadar tattalin arzikin na Turkiyya kan basussukan da ake bin kasar da faduwar darajar kudin kasar, zai zamanto takaitacce, inda mai yiwuwa Burtaniya ta fi kowacce kasa makuwa daga wannan matsala, saboda bankunan kasar da dama, su suka fi ba kasar ta Turkiyya basussuka, kamar yadda masanin tattalin arziki a bankin Deutsche, Oliver Harvey ya fada.
Facebook Forum