Kasuwannin hannayen jarin nahiyar Asiya sun dan daga sama a yau Talata, a yayin da masu saka jari suka wayi gari da kyakkyawan labarin ci gaban da kamfanonin China suka samu, kuma a daidai lokacin da ake fama da annobar coronavirus.
Kamfanin Hang Seng na Hong Kong ya daga sama da maki 328 wato kashi 1.5 bisa dari, yayin da hannun jarin Shanghai ya sami ribar daya bisa goma.
To sai dai hannayen jarin Nikkei na Japan da A.S.X na Australia sun karkare ranar tare da yin kasa, inda Nikkei ya fadi da kasa da kashi 1 bisa dari, A.S.X kuma yayi kasa da kashi 2 bisa dari.
Hannayen jarin Turai sun sami ci gaba da safiyar yau, yayin da kasuwar mai ma ta dan sami ci gaba a farashin man, bayan faduwa mafi muni da tayi kwanan nan da ba a ga irinta ba tun a shekarar 2002.
Facebook Forum