Koriya ta Kudu ta ce zata bada tallafin kudin gaggawa ga ‘yan kasar da dama a zaman wani yunkuri na habbaka tattalin arzikin kasar, a daidai lokacin da ake fuskantar annobar cutar coronavirus a fadin duniya.
A lokacin wata ganawa da wani kwamiti na musamman a yau Litinin, shugaban Koriya ta kudu Moon Jae-in ya sanar da cewa, gwamnatinsa zata biya kusan dala $820 (kwatankwacin naira 300,000) ga kowanne gida (iyali) amma banda wadanda kudin shigarsu ya haura kashi 30 cikin 100, abinda ya bada jimlar dala biliyan $7.4 da gwamnatin zata kashe.
Shugaba Moon ya ce wannan tamkar wata diyya ce ga ‘yan kasar da suka jure wa matakan zama a gida tsawon makonni don dakile yaduwar annobar coronavirus, cikin matakan har da killace jama’a da kuma nisantar juna.
Koriya ta Kudu tana da mutum 9,661 da suka kamu da cutar coronavirus ya zuwa yau Litinin, inda mutum 159 suka riga mu gidan gaskiya, kana mutum 5,228 suka warke daga cutar.
Kasar dai ta sami yabo daga kasashen duniya, akan yadda take gudanar da gwajin cutar ga daruruwan mutane a kowacce rana, wanda hakan ya taimaka matuka wajen rage yaduwar cutar.