Kasuwannin hannayen jarin Amurka sun yi sama da kashi 3.4 cikin 100 zuwa yammacin jiya Laraba, saboda wasu matakan da aka dauka.
Ciki akwai matakin da gwamnatin Trump ta dauka na bai wa masu sayen hannayen jari kwarin gwiwa ta wajen wani shirin sake farfado da tattalin arziki.
Da kuma matakin da Bernie Sanders ya dauka na kawo karshen yakin neman zaman dan takarar shugabancin kasa.
Sanders dai ya yi alkawarin kara wa manyan kamfanoni haraji idan har aka zabe shi.
Haka ma shirinsa na tsarin kiwon lafiya na bai daya, shima ya haddasa tsoron yiwuwar kara wasu dokoki da ka iya janyo kashe kudi mai yawa kuma riba kadan.
Dukkan manyan hannayen jari sun yi sama a dai-dai lokacin da aka rufe kasuwar jiya Laraba.
Kasuwar Dow Jones ta cira da kashi 3.44 cikin 100.
Ita kuma S&P-500 ta yi sama da kashi 3.40, sai kuma NASDAQ da ta rufe da Karin kashi 2.58.
Facebook Forum