Daga cikin malamai 16,898 da aka kyasta cewa za a tantance a karkashin shirin dake hangen tayar da komadar da ake fama da ita a makarantun sakandare hukumomi sun bayyana cewa 16,647 ne aka yi nasarar tantancewa.
Bayan shafe makwanni 3 cif na gudanar da wannan aiki rahoton bincike ya yi nuni da cewa kasa da kashi 40 daga cikin 100 na malaman kawai suka cacanci aikin koyarwa yayin da wasun ke da dama-dama a cewar Ibrahima Sidi, daya daga cikin jami'an ma'aikartar ilimi na makaratun secondary.
Wata jarabawara makamanciyar wannan da aka gudanar a 2017 ta yi sanadiyar korar daruruwan malaman firaimari daga aiki, dukkansu ‘yan kwantaragi bayan da aka gano su da rashin yin wani abin a zo a gani.
Sai dai a wannan karon hukumomin ilimi a matakin Secondary sun ce ba su da niyyar daukan irin wannan mataki.
A gaban masu ruwa da tsaki a sha’nin ilimi na gwamnati da na kungiyoyi masu zaman kansu ne aka gabatar da wannan sakamako na jarabawar tantance malaman saboda haka muryar Amurka ta nemi jin matsayin kungiyar malaman secondary ta SYNAFCES.
Malan Jariri Labo Saidou shine sakataren ta, ya kuma ce ya kamata idan aka dauki mutune aiki kamar 'yan kwantaragi, kamata ya yi gwamanti ta dauke alkawarin daukan su aikin din-din-din kuma a biyasu akai-akai ba sai bayan an ja tsawon kwanaki ba.
Amfani da takardar kammala karatu ta jabu na daga cikin matsalolin da aka gano a jerin abubuwan da ke haddasa koma bayan da ake fama da shi a fannin ilimi, abin da ke kara fayyace girman wannan matsala.