Kasashe da dama a fadin duniya na daukar matakai domin sassauta dokar hana zirga-zirga da suka saka saboda hana yaduwar cutar coronavirus.
Hukumomi a kasar Jamus sun bai wa wasu kananan shaguna damar budewa don ci gaba da kasuwanci yau Litinin, amma dai dokar bada tazara a tsakanin jama’a na ci gaba da aiki.
A kasar Albania, daruruwan masu kananan sana’o’i sun fito don gudanar da kasuwancinsu a yau Litinin a karon farko bayan tsawon wata daya. Haka kuma an ba masu kamun kifi da sana’ar abinci damar komawa bakin sana’o’insu.
A kasar Sri Lanka kuwa an sassauta dokar a kusan kashi biyu cikin uku na kasar, ana kuma shirin cire dokar a sauran bangarorin kasar nan da zuwa ranar Laraba.
Dalibai a kasar Norway sun koma makarantu a yau Litinin, su kuwa na kasar Denmark na shirin komawa makaranta a ranar Laraba.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesu, ya ce ya samu kwarin gwiwa daga kasashen dake shirin sassauta dokar takaita mu’amala, amma ya yi gargadin cewa yana da muhimmanci a sassauta matakan sannu a hankali.”
Facebook Forum