Kasar Turkiyya ta bada sanarwar cewa tana taimakawa kurdawa daga Iraqi su tsallaka cikin Syria, domin su kai ‘dauki’ ga mayakan sakan kurdawa da suke fafatawa da mayakan sakan kungiyar ISIS, wadanda suke dannowa kan garin Kobani.
Sanarwar da ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya bayar, ta zo ne a dai dai lokacinda Amurka take cewa ta samar da makamai da albarusai da kuma kayan jinya ko kiwon lafiya, da hukumomin kurdawa a Iraqi suka samar, ta wajen wurga musu kayan daga jiragen sama a kudancin yankin dake kan iyakar Syria da Turkiyya.
Minista Cavusoglu`bai yi wani karin bayani kan Karin tallafi da Turkiyya take baiwa kungiyar mayakan sakan kurdawan da ake kira Peshmerga ba. Sai dai yace hukumomin kasar da suke Ankara, suna son kawarda duk wata barazana akan yankin kan iyakarta, saboda haka tana hada kai da rundunar taron dangin da Amurka take yiwa jagoranci a yaki da kungiyar ISIS.