Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Rasha Zata Fice daga Kotun Manyan Laifuka Na Kasa da Kasa ko ICC


Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun yi Allah wadai da umarni da shugaban Rasha Vladmir Putin ya bayar na fidda Rasha daga kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ta ICC, abin da suka kira da mataki na son zuciya da kuma shu’umanci ga shari’a.

Wata dokar Rome ce dai ta kafa wannan kotun a shekarar 1998. Putin ya sanya hannu a kan yarjejejniyar amincewa da kotun shekarar 2000 amma Rasha bata tabattar da hallacinta ba.

Wata mace da ake kira Tanya Lokshina, ‘yar kungiyar rajin kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch dake a birnin Moscow ta fada a wani sakonta na email cewa ficewar Rasha daga kotun ICC wata alama ce dake nuna yanda Rasha bata mutunta hadin kai ga shari’ar kasa da kasa da kuma hukumomin tabattarda adalaci na kasashen duniya.

Lokshina tace sanya hannun da Rasha ta yi akan wannan dokar kafa kotun tun shekara da shekaru, na nuna amincewarta da kuma yin aiki da kotun.

Yanzu kuma Rasha ta fito karara tana cewa bata son abin da kotun ke yi kuma tayi watsi da tsarin shari’a kasa da kasa.

Wannan matakin ficewa daga kotun ta duniya da Rasha tayi dai ya faru ne kwana daya bayanda wani rahoto na kotun ya la’anci mamayen da rasha din tayi wa yankin crimea na kasar Ukraine.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG