Anga masu zaben cikin farin ciki suna fitowa daga rumfunan zabe da yatsu da suka tsoma cikin tawada, alamar cewa sunyi zabe, wasu da dama daga cikinsu wannan ne karon farko da suka taba yin zabe a rayuwarsu.
Kimanin 'yan kasar milyan 32 ne aka yiwa rijista domin su zaba daga cikin fiyeda 'yan takara dubu shida, wadanda suka yi takarar wakilci a majalisun tarayyar kasar biyu da kuma na yankunan kasar daban daban. Jami'an aikin zabe suka ce kusan kashi 80 cikin dari na wadanda aka yiwa rijista ne suka fito domin zaben.
Sakataren harkokin wajen Amurka John kerry, ya taya jama'ar kasar murna, ya kira zaben "shaida ta irin bajinta da sadaukar da kan jama'ar kasar cikin shekaru masu yawa."
Mr. Kerry yace "zaben muhimmin mataki ne na ci gaba," duk da cewa bai cika 10 ba.
Ahalinda ake ciki kuma,sakamakon farko farko na zaben da aka yi a Croatia ya nuna jam'iyyar 'yan hamayya mai ra'ayin rikau HDZ a takaice, ta lashe kimanin kujeru 60 a majalisar dokokin kasar, yayinda jam'iyyar Social Democrat mai mulkin kasar ta sami kujeru 53 a zaben 'yan majalisa da aka yi jiya l
Lahadi.