Ministan harkokin cikin gida na Italiya, Matteo Salvini, ya ce ya kamata hukumomin Libiya su yi aikin su na cetowa, da taimakawa, da kuma maida bakin kasashen su, kamar yadda suka saba yi na tsawon wani lokaci, ba tare da jirgen kungiyoyi masu zaman kansu sun dame su ba ko sun tada wata fitinar, Ya kuma ce “an rufe tashoshin jiragen ruwan Italiya kuma zasu kasance a rufe ga masu taimakawa masu safarar mutane.
Jiya Lahadi, wata ƙungiyar agaji da ake kira Spanish Proactiva Open Arms, ta ce dogarawan tsaron tekun Italiya sun sami sakon gaggawa daga wasu jiragen ruwa guda 6 dauke da kusan mutane 1,000, amma kasar Italiya ta fadawa kungiyoyin agaji irinsu Proactiva cewa kada su damu ba a bukatarsu.
A maimakon aikin ceton, sai dogarawan tsaron bakin tekun Italiya suka sanar da Libya, suka kuma danka aikin ceton ga takwarorin aikinsu na kasar ta Libya.
Facebook Forum