Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar India Ce Ta Fi Hadari Ga Rayuwar Mata


'Yan mata 'yan makaranta suna gangami akan yadda ake yiwa yara mata fyade a India
'Yan mata 'yan makaranta suna gangami akan yadda ake yiwa yara mata fyade a India

Jiya Talata Gidauniyar Thomas Reuters ta fitar da sakamakon wani bincike inda ta ayyana kasar India a matsayin kasar da ta fi hadari ga rayuwar matacikin kasashe 193 na Majalisar Dinkin Duniya

An ayyana kasar India a matsayin wuri mafi hadari ga rayuwar mata a duniya, a wani bincike da masana akan batutuwan da suka danganci mata suka gudanar.


Binciken da gidauniyar Thomas Reuters ta fitar da samakonsa a jiya Talata, ya tambayi masana 550 a kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya 193 a kan wani wuri yafi hadari ga rayuwar mace, a kan kiwon lafiya, da tattalin arziki da muggan al’adu da cin zarafi ta keta haddin su da kuma safarar mata.


Kasashen da suke biye da India wurin cutar da mata sune Afghanistan da kuma Syria da yaki ya daidaita. Sai kuma Somalia ta hudu yayin da Saudi Arabia take bi mata a matsayin na biyar.


Kasashe da suke bi musu kuma sun hada Pakistan da Demokaradiyyar Jamhuriyar Congo da Yemen da Nigeria da kuma Amurka wacce take ta cikon goma.

Amurka ce wata kasar turai da take cikin kasashen dake cin zarafin mata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG