Gwamman kasashe ne suke aiki don magance barkewar cutar coronavirus, yayin da adadin mutanen da cutar ta kashe a duniya ya haura 3,000, ciki har da mutane biyu a Amurka.
Koriya ta Kudu ta sanar da samun karin mutane kimanin 600 da suka kamu da cutar a yau Litinin, yayin da shugaban wata kungiyar addinin da ke da alaka da galibin wadanda suka kamu da cutar ya nemi afuwa.
Jami’ai sun bukaci masu gabatar da kara su duba yiwuwar tuhumar shugabannin kungiyar da laifin kisa, saboda sun ki ba da hadin kai a kokarin da gwamnati ke yi na dakile cutar.
A yau ake sa ran shugaban Amurka Donald Trump zai gana da mataimakinsa Mike Pence wanda ke jagorantar yaki da cutar, tare da wasu shugabanin kamfanonin hada magunguna.
Ya zuwa yanzu dai an tabbatar da cewa mutune sama da 80 sun kamu da cutar a Amurka, ciki har da mutane 2 da suka mutu a yammacin jiya Lahadi a jihar Washington. Jami’ana kiwon lafiya sun ce akwai yiwuwar cutar ta dau tsawon makonni ta na yawo cikin al’umma, kafin a gano ta.