Baya ga wannan matsalar rashin samun isassun kudaden tafiyar da manyan makarantun da kuma rashin samun kulawa mai kyau ga malaman dake koyarwa a yanzu na ci gaba da yin tasiri wajen rashin samun ingantaccen ilimi mai zurfin a Najeriya.
Farfesa Abdullahi Bala mataimakin shugaban Jami'ar kimiyya da fasaha ta gwamnatin Najeriya dake birnin Minna yayi karin haske akan yadda Jami’o’in kasar ke fuskantar wannan matsala, yana mai cewa, rashin kayan aiki da isassun malamai na kawo koma baya ga sha’anin ilimi a Jami’o’in kasar.
Wannan dai wata babbar matsalace da masana harkokin ilimin ke ganin tana matukar bukatar kulawar gaggawa daga gwamnatin Najeriya.
Ahalin da ake ciki dai maitaimakin shugaban Jami’ar kimiyyar ta Minna Farfesa Abdullahi Bala ya ce, duk da yake suna samun dalibai ‘yan asalin kasashen waje dake zuwa karatu a Jami’o’in kasar, amma basu iya dauko malamai ‘yan kasashen waje domin koyarwa a Jami’o’in.
A bana dai Jami'ar kimiyya da fasaha ta gwamnatin Najeriya dake Minna ta yaye dalibai 5,049 a fannoni daban-daban na saukar karatu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru batsari: