Cikin abubuwan da kungiyar shugabannin jami'o'in Afrika ta Yamma suka sa gabansu sun hada da binciken kimiya da fasaha da zamantakewar jama'a da yadda gwamnatoci da kamfuna zasu gudanar da sakamakon binciken domin cigaba.
Farfasa Abdullahi Yusuf Ribado sakataren kungiyar kuma shugaban Jami'ar Jihar Jigawa yace jami'a ba'a yita don kawai a koyas da dalibai su samu digiri ba. Ana son a jami'a a samu sabon ilimi. Yace shi ko sabon ilimi ba'a samunshi sai an yi bincike. Bincike kuma baya yiwuwa sai da kudi
Farfasa Ribado yace suna son su wayarwa masu jami'o'in kawuna cewa lallai bincike yana da mahimmanci. Bincike ne zai sa kasashe su cigaba. Amma binciken ba zai yiwu ba idan ba'a bada isasshen kudi ba. Suna anfani da dangantakar da suke da ita da kungiyar ECOWAS domin ta taimaka wurin fadakar da shugabannin kasashen akan wannan kalubale da jami'o'i ke fuskanta.
A cikin makon nan ne ita Jami'ar Jihar Jigawa tayi bikin daukan dalibai karo na ukku su kimanin dari tara. A lokacin bikin ne sarkin Hadeija ya kira gwamnatoci su dingi ba jami'o'i kashi hamsin na kasafin kudinsu kowace shekara.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.