Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kanye West Yace Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasa A 2024


Shaharraran mawaki Kanye West
Shaharraran mawaki Kanye West

Shaharraran mawakin Amurka Kenya West wanda ya canza sunansa zuwa Ye a hukumance, wanda ya tsaya takara a shekarar shugaban kasar Amurka a 2020 ya ce zai sake tsayawa takara ya kuma taka rawa a zaben 2024.

Kanye ya kuma nemi taimakon mai ra'ayin mazan jiya Milo Yiannopoulos don taimakawa kan yakin neman zabensa.

A cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a kan Twitter ranar Lahadi, Kanye ya ce: "Wannan Milo ne, yana kuma aiki kan kamfen dina."

Bidiyon, wanda West ya ce Yiannopoulos na aiki kai kan yakin neman zabensa, ya zo ne a daidai lokacin da aka dawo wa mawakin da shafin Twittansa bayan an dakatar da shi daga manhajar sakamakon munanan kalamai na nuna kyama da Yahudawa da ya yi a watan jiya.

Ko da aka aka tambaye shi: "Shin wannan sanarwar ce?"

Milo ya yi dariya kamin ya amsa: “Ina tsammanin hakan ne. Na gode kuma na karba.”

Sanarwar ta zo ne bayan abokin Kanye, shahararran mawaki Akon, a kwanan nan ya yi hasashe cewa abin mamaki da abokin nasa ya yi a baya-bayan nan - ciki har da wasu kalamai na nuna kyamar Yahudawa, wani bangare ne na yunkurin lashe zabe a kan masu kada kuri'a wanda idan ba haka ba, zai goyi bayan yunkurin Donald Trump na komawa ofishin shugaban kasa a shekarar 2024.

Da sanyin safiyar Lahadi, mawakin ya wallafa sako a shafinsa na Twitter don ganin ko an dawo da shafinsa na Twita tun lokacin da Elon Musk ya karbi ragamar kamfanin.

"Gwaji Gwaji Gwaji don in gani ko har yanzu shafin Twitta dina na zaune a toshe," West ya rubuta wa mabiyansa na kusan miliyan 32.

Musk, wanda ya sayi kamfanin a kan dala biliyan 44, ya ce a watan da ya gabata ne aka dawo da shafin twittan Kanye tun kafin sayen kamfanin kuma ba a tuntube shi ba kafin a dawo da shi.

XS
SM
MD
LG