Irin wadan nan cin hanci a matakai daban daban na taka rawa gaya wurin kara tabarbarar da alamura a cikin kasa.
Kwamred Abubakar Abdulsalam shugaban wata kungiya dake rajin yaki da cin hanci a cikin kasa yace a gwamnatin ta yanzu 'yansanda, sojoji da ma'aikata ko na fararen hula a ofisoshi duk suna neman na goro a hannun jama'a kafin su yi aikinsu. Yace lokacin da ake karancin mai a jihar Adamawa sojoji ne suke korar mutane a gidajen mai su shiga da manya manyan duram a cika masu da mai su je su sayarwa masu sayar da man a kasuwar bayan fage. Suna anfani da rigunan sarki su cuci mutane.
Shi ma Kwamred Nasiru Kabir yace kananan cin hanci su ne babban illa a kasar. Ciin hancin nan babu babba babu yaro. Yace dama da cin hanci karami ake farawa kafin ya zama babba. Yace idan mutum ya je asibiti mai kula da mutum ba zai saurareshi ba sai an bashi wani abu. 'Yansanda akan hanya kirikiri suke karbar nera goma zuwa ashirin hannun mutane. Mai laifi sai ya wuce domin ya basu wani abu. Idan gwamnati bata tashi tsaye ba to ba karamin illa zai dinga yiwa kasar ba da jama'arta tare da dagulewa mutane alamuransu.
Ga karin bayani.