Gwamnatin Amurka za ta biya dala biliyan daya da miliyan dari tara ga kamfanin sarrafa magungunan Amurka Pfizer da kamfanin kere-kere na kasar Jamus BioNTech SE, akan allurar rigakafin cutar COVID-19 guda miliyan 100, idan aka tabbatar da ingancin ta.
A jiya laraba kamfanonin sun ce, sun kammala wata yarjejeniya da hukumar lafiya da ayyukan jin dadin jama'a ta Amurka, tare da Ma'aikatar Tsaron Amurka don samar wa hukumomin rigakafin da suke sarrafawa da hadin guiwa, wani mataki na baya bayan nan a yarjejeniyar da aka cimma da kamfanoni domin samar da allurar rigakafin.
Sakataren hukumar Lafiya da kula da jin dadin Jama'a ta Amurka Alex Azar ya shaidawa tashar labarai ta Fox News cewa, Amurka za ta iya sayen karin alluran rigakafi guda miliyan 500, idan aka tabbatar da matukar “ingancin su da kuma tasirin su.”
Yarjejeniyar da aka bayyana a jiya Laraba, wani bangare ne na shirin Shugaba Donald Trump da ake kira “Operation Warp Speed”, wanda ake fatan samar da allurar rigakafi miliyan 300 da aka amince da ingancin su, nan da 20 ga watan Janairu na shekarar 2021.
Facebook Forum