Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kalubalanci jami'an sojin Nigeriya da su maida hankali kan yaki da ta'addanci da ke addabar kasar maimakon shiga harkokin siyasa.
Gwamnan ya bayyana hakkan ne lokacin bude wani taron babban hafsan sojan kasa na Nigeriya a garin Maiduguri dake shiyyar arewa maso gabashin Kasar.
Babban hafsan sojan kasan Nijeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce, sun samu gudanar da zabubbuka ba tare da samun wani cikas ba, musamman ma a zaben da aka gudanar a jihar Edo, ya kara da cewa Shirin “Operation Safe Conduct” da aka aiwatar lokacin zabe a jihar Edo shaida ne, kuma yana yaba wa jami’an sojan kasar.
A jawabin da Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya gabatar ya fara ne da yaba wa jami’an sojan Najeriya kan yadda suke gudanar da aikinsu, ya ce, amma ya kamata jami’an sojan kasar su mayar da hankali kan yaki da ta’addanci.
Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Biu cikin sauti:
Facebook Forum