Wasu majiyoyi biyu sun fadawa AFP cewa, an gano karin wasu gawarwaki bayan harin wanda aka kai a ranar Juma’a .
Karin wadanda aka gano, sun hada da ‘yan sanda 12, sojoji biyar, da wasu ‘yan sintiri na civilian JTF hudu da kuma fararen hula tara a cewar kamfanin dillancin labaran.
Gabanin gano karin wadanda suka mutun, majiyoyin sun fadawa AFP cewa, wasu mahara sun afkawa ayarin gwamnan jihar Borno, Prof. Babagana Umara Zulum a yankin garin Baga da ke kusa da yankin Tafkin Chadi.
Ko a watan Yulin da ya gabata, ayarin motocin gwamnan ya fada tarkon maharan a kusa da garin na Baga, lamarin da ya tilasta masa janye ziyarar da ya yi shirin kai wa a lokacin.
Mayakan ‘yan ta’adda na ISWAP ta yammacin Afirka da ke da alaka da kungiyar IS, sun dasa matsugunansu a tsibiran da ke yankin Tafkin Chadi – yankin da ya zama masu tunga.
A baya-bayan nan kungiyar ta zafafa hare-haren da take kai wa akan dakaru da fararen hula a yankin.
Rikicin Boko Haram, wanda aka kwashe sama da shekara goma ana yi a arewa maso gabashin Najeriya ya halaka mutum dubu 36 kana ya tilastawa sama da mutum miliyan biyu ficewa daga muhallansu.
Facebook Forum