Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KAMARU: Yan Boko Haram Na Cigaba Da Tuba


Mayakan boko haram da suka tuba
Mayakan boko haram da suka tuba

Kamaru ta mayar da gine -ginen jama'a da ke kan iyakarta da arewacin Najeriya zuwa matsugunan tsoffin mayakan Boko Haram da suka tuba. Daruruwan 'yan Boko Haram na ficewa daga kungiyar da suka hada da sama da dari biyu ranar Lahadi.

Kamaru ta ce cibiyar ta sake daidaita sawu da tsugunarwa ko DDR,a Meri, wani gari na arewacin kasar da ke kan iyaka da Najeriya, a yanzu ta zame mastuguni kuma tana da tsoffin mayakan Boko Haram kusan 1,500. Makonni uku da suka gabata, cibiyar tana da tsoffin mayaka kusan 750.

Jami'an DDR a Meri sun ce ran Talata mafi yawan tsoffin mayakan 237 da suka isa wannan makon sun hada da mata da yara. Darurruwan su tsoffin mayaƙan Boko Haram ne, duk sun gaji, ba su da lafiya kuma suna jin yunwa, in ji jami'ai.

Francis Fai Yengo, daraktan DDR na kasar, ya ce shugaban Kamaru Paul Biya ya ware kudade don gina cibiyar DDR da za ta iya karbar bakuncin tsoffin mayaka 1,500 a Meme, wani gari da ke arewa da kan iyaka da Najeriya. Ya ce Kamaru na godiya cewa mayakan da dama na tserewa daga sansanin Boko Haram.

Francis Fai Yengo
Francis Fai Yengo

Shima Oumar Bichair, darektan cibiyar DDR a Meri, ya ce cibiyar ta riga ta cika kuma ya kamata Najeriya ta nemi matsuguni wa mayaka yan Najeriya don su koma gida.

Alidou Faizar mai shekaru talatin da uku ya ce ya fice daga sansanin Boko Haram a dajin Sambisa da ke kan iyakar Kamaru da Najeriya.

Ya ce ya gaji da kisa da sace -sace kuma Boko Haram ta yi alkawarin inganta yanayin rayuwarsa lokacin da ya shiga kungiyar shekaru 3 da suka wuce, amma yanzu ya ma fi talauci fiye da da, kuma yana fama da nadamar laifuffukan, yana tuna masa laifukan da ya aikata. Ya kara da cewa zaman lafiya ba shi da kima.

Faizar ya ce burinsa shine ya koma Abadam, wani gari a jihar Borno ta Najeriya. Kamaru ta ce kusan 900 daga cikin tsoffin mayakan 1,500 a Meri 'yan Najeriya ne.

XS
SM
MD
LG