Haka ma ita kasar Kamaru din zata dinga aika da kayanta domin sayarwa ba tare da biyan haraji ba.
Jakadiyar kasashen nahiyar Turai Francois Collett ta yaba da yarjejeniyar da kasar Kamaru ta cimma da kasashen Turai. Tace lamarin zai taimakawa kasar ta Kamaru musamman wajen farfado da tattalin arzikin kasar.
Alhaji Tanimu Bafan wanda ya kasance babban dan kasuwa yace yarjejeniyar zata kawowa harkokin kasuwanci cigaba. Kawar da haraji ma kayan kasar a Turai zai taimaka. Yace kamar ayabar Kamaru idan sun kaita Turai suna biyan haraji. Ta bangaren talakawa, magunguna da ake shigowa dasu daga Turai zasu yi araha, lamarin da zai rage masu radadin talauci.
Ga rahoton Awal Garba da karin bayani.