Babban jami’in kula da harkokin cututtuka na Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, wasu daga cikin kalaman da Trump ya furta a jawabansa dangane da cutar coronavirus na iya haifar da rashin fahimta akan hakikanin al’amura game da cutar.
Dr. Anthony Fauci, shine shugaban cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasa da ake kira NIAID a takaice, ya kasance sanannen suna sakamakon jawaban fadar shugaban kasa akan cutar coronavirus.
A wata hira da mujallar ‘Science’ ta yi da shi, Fauci ya ce a yayin da bai amince da wasu kalaman Trump ba, zai rinka bayyana lamarin a wani yanayi na dabam.
Fauci ya ce “Trump yana daukar tashi hanyar, yana da nashi tsarin. To amma akan wasu muhimman al’amura, ya kan saurari abinda nake cewa”.
Sai dai babu wani kwakkwaran abu da likitan zai iya yi idan Trump ya furta kalaman da ba daidai ba.
Ko a wani taron manema labarai a makon da ya shige, Trump yayi furucin da ba gaskiya ba, na cewa hukumar kula da abinci da magunguna ta amince da yin amfani da wani maganin masassarar cizon sauro domin kula da masu cutar coronavirus.
Facebook Forum