Sojojin Burkina Faso, wadanda su ka yi juyin mulki ranar Jumma'a, sun ce zasu kafa gwamnatin hadin kan kasa, wadda zata kula da shirye-shiryen komawa kan tafarkin dimokaradiya bayan hambare dadadden Shugaban kasa Blaise Compaore.
Wani dan takaitaccen bayanin da sojojin su kayi da daren jiya Lahadi, ya ce za’a amince da dukkannin fannonin shirye-shiryen komawa kan tafarkin dimokaradiyar ne ta wajen samun yardar sassan jama'a sosai. To amma ba’a yi cikakken bayani ba.
Sanarwar ta jiya Lahadi, wadda aka yi a birnin Ougadougou, ta biyo bayan rudanin da aka shafe sa'o'i ana samu, kan ko wa zai jagoranci wannan matalauciyar kasar Yammcin Afirka mai mutane miliyan 17.
Jim kadan da murabus din da aka matsa ma Mr. Compaore ya yi, wasu manyan jami'an soja biyu sun yi ta ikirarin jagorancin kasar. To amma jiya Lahadi sojoji sun nada daya daga cikinsu, mai suna Laftana-Kanar Yakuba Isaac Zida, ya jagoranci gwamnatin wuccin gadin.