Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jordan Ta Ce Ta Cafko Wasu Abubuwa Masu Firiya Da Suka Shiga Sararin Samaniyarta

An ga wasu abubuwa masu firaye a sararin samaniyar Amman bayan da Iran ta harba jiragen yakin Isra'ila
An ga wasu abubuwa masu firaye a sararin samaniyar Amman bayan da Iran ta harba jiragen yakin Isra'ila

Iran ta harba jirage marasa matuka masu tarwatsewa tare da harba makamai masu linzami kan Isra'ila da yammacin jiya Asabar - harin da ta kai na farko kai tsaye a kan yankin Isra'ila a matsayin ramuwar gayya da ke kara tsananin barazana a rikicin yankin. 

Wata sanarwar da majalisar ministocin kasar ta fitar a ranar Lahadin ta ce kasar Jordan ta cafke wasu abubuwa masu firiya da suka shiga sararin samaniyarta da daren Asabar domin tabbatar da tsaron lafiyar 'yan kasar.

Iran ta harba jirage marasa matuka masu tarwatsewa tare da harba makamai masu linzami kan Isra'ila da yammacin jiya Asabar - harin da ta kai na farko kai tsaye a kan yankin Isra'ila a matsayin ramuwar gayya da ke kara tsananin barazana a rikicin yankin.

IRAN-MILITARY/
IRAN-MILITARY/

Majiyar tsaron yankin biyu ta bayyana cewa, kasar Jordan da ke tsakanin Iran da Isra'ila, ta shirya matakan kariya ta sama domin dakile duk wani jirgi mara matuki ko makami mai linzami da ya keta kasarta.

Sanarwar da majalisar ministocin kasar ta Jordan ta fitar ta kara da cewa, "Wasu baraguzai sun fadi a wurare da dama a lokacin ba tare da yin wani gagarumin barna ko jikkata ga 'yan kasar ba.

Tashar talabijin ta Channel 12 ta kasar Isra'ila ta bayyana cewa jiragen yakin Amurka da na Birtaniyya sun yi luguden wuta kan wasu jiragen da aka harba zuwa Isra'ila a kan iyakar Iraki da Siriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG