Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

John Kelly Ya Saka Hannu a Wata Doka Da Ta Soke Tsohon Shirin Gwamnatin Obama


Masu zanga zangar kin dokar Trump ta hana baki a Amurka
Masu zanga zangar kin dokar Trump ta hana baki a Amurka

An Soke Shirin Shugaba Obama na dakatar da mayar da mutanen da ke zaune a Amurka ba bisa ka'ida ba zuwa kasashensu.

Hukumar tsaron cikin gida ta Amurka ta soke wani shiri da tsowuwar gwamnatin da ta gabata ta Obama tayi, wanda ya taimaka wajen dakatar da mayar da mutanen da ke zaune Amurka ba bisa ka’ida ba kasashensu, wadanda suke da 'ya'ya ‘yan Amurka.

A wata sanarwa da aka fitar jiya Alhamis, Sakataren Ma'aikatar Tsaron cikin Gida ta Amurka, John Kelly, ya saka hannu a wata doka da ta soke wancan shiri na gwamnatin Obama.

Tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama, ya gabatar da shirin ne a shekara ta 2014, amma wata kotun tarayya ta dakatar da shirin bayan da wasu jihohi 26 suka yi kukan cewa Obama ya wuce gona da iri, wajen kare wasu mutanen da ke zaune a Amurka ba bisa ka’ida ba.

Yaki da mutanen dake zaune a Amurka ba tare da takardu ba, na ‘daya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin Trump ta yi alkwarin aiwatarwa lokacin yakin neman zaben ta.

Haka kuma sanarwar ta ce ba a taba shirin nan da ya baiwa yaran da aka shigo da su Amurka ba bisa doka ba, damar yin karatu ko aiki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG