A Brazil, sama da mutane dubu sun yi maci daga wata unguwar marasa galihu a birnin Rio de Janeiro a jiya Lahadi, don nuna rashin amincewarsu da kisan gillar da aka yiwa wata bakar fata 'yar majalisa, kuma 'yar gwagwarmaya kare hakkin bil adama, Marielle Franco.
Wadanda suka shirya macin sun yi amfani na'urorin kara sauti suna kuwa suna fadin "muryarta ba zata mutu ba", yayin da suke maci ta kan babban titin birnin.
Wasu yan siyasa da suka shiga cikin macin sun ce, in an kashe Franco ne don mutane su ji tsoro su yi shuru, toh za a ga akasin haka, kuma irin kwarin gwiwarta zai mamaye kasar Brazil.
A ranar Laraba da ta shige ne aka harbe Franco da direbanta yayin da suka bar wurin wani taron da aka yi domin taimakawa mata bakar fata.
Franco mamba ce a majalisar birnin Rio, kuma mai fafutukar kare hakkin marasa galihu ce, ta dade tana yakin kare 'yancin tsiraru, kan zargi da ake yiwa yan sanda na cin zarafin mutane a unguwannin marasa karfi.
Shuagabn Brazil Michel Temer ya zuba sojoji su kula da tsaron a birnin Rio saboda kukar da yake samu daga kungiyoyin kare hakkin bil adama a kan cin zarafi mai tsanani har da mutuwa da yan sanda ke yiwa mutane.
Masu sukar lamiri sun ce zuba sojojin bai yi wani tsairi ba.
Facebook Forum