Hukumar ta ce rashin amfani da gargadi na ambaliyar ruwa a bana daga gwamnatocin jihohi ya ta’azzara lamuran da za a ma iya kauce mu su.
Shugaban hukumar ta NIHSA Clement Nze ya ce nan da wata daya gagarumin ruwan koguna zai gangaro daga kasashen Benin, Cote d’ivoire, Guinea, Mali, Burkinafaso, Chad da Kamaru zuwa Najeriya don haka akwai bukatar daukar matakan kare irin illar ambaliyar ruwa da hakan zai kawo.
Nze ya bukaci mutane su gujewa gina gidaje kan hanyoyin ruwa, kazalika gwamnatoci su tabbatar da samar da magudanan ruwa.
Cikin shawarar da hukumar ta bayar har da gina madatsun ruwa don tara ruwan a waje daya da hakan zai hana malalar ruwan cikin gidajen jama’a.
Hukumar ta baiyana jihohi 15 da ke cikin yankunan da a ke fargabar samun ambaliyar da su ka hada da Adamawa, Abia, Bauchi, Delta, Jigawa, Neja, Lagos, Edo, Kuros Riba, Oyo, Enugu, Kebbi, Imo, Nassarawa da Abuja.
Ga dai rahoton Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja:
Facebook Forum