Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihohin Da Aka Samu Bullar Coronavirus a Najeriya


Ministan Lafiya na Najeriya, Dr Osagie Ehanire
Ministan Lafiya na Najeriya, Dr Osagie Ehanire

Hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC, ta tabbatar da samun karin mutum goma da suka kamu da cutar coronavirus a kasar.

Bayanan da hukumar ta wallafa a shafinta na yanar gizo a ranar Asabar, sun nuna cewa adadin masu dauke da cutar ya kai 22.

Sai dai hukumar ta nuna cewa an sallami mutum biyu.

Wata sanarwa da Ministan Lafiya Dr. Osagie Ehanire ya wallafa a shafinsa na Twitter ta nuna cewa, uku daga dikin mutanen a Abuja aka same su, yayin da sauran mutum bakwai kuma a Legas.

Da ma Legas ce jihar da cutar ta fara bulla bayan da wani dan kasar Italiya ya shiga birnin da ita.

A halin da ake ciki, Legas na da mutum 16, Ekiti daya, Ogun biyu yayin da babban birnin kasar yake da mutum uku a cewar Ministan.

Ya kuma kara da cewa, dukkan wadanda aka samu da cutar na cikin yanayi na koshin lafiya tare da samun kulawar da ta dace.

Akwai dai rahotanni da ke nuna cewa an samu bullar cutar a wasu jihohin Najeriyar, amma hukumomi ba su tabbatar da hakan ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG